Use APKPure App
Get Sheikh Jafar - Sharhin Kashf ush-Shubuhaat Mp3 old version APK for Android
Wannan ứng dụng yana dauke da Fassarar Sharhin Kashf USH-Shubuhaat Mp3 tuyến
Assalamu Alaikum
Wannan app yana dauke da Fassarar Sharhin Kashf ush-Shubuhaat Mp3 Offline na Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam da Sheikh Abubakar Husani, shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake
Allah ya sakawa Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya kuma jikansa.
Domin samun sauran apps na Sheikh Jafar da sauran manyan malamai na sunnah duba (rrnapps) free Hausa Islamic apps dake cikin play store
Don Allah a taimaka a yi sharing ta facebook, whatsapp, twitter da sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su amfana.
Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.
*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam
An haifi marigayi SheikhJa'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma
Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Sharhin Kashf ush-Shubuhaat, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar
(Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna
Last updated on Nov 3, 2019
Minor bug fixes and improvements. Install or update to the newest version to check it out!
Được tải lên bởi
Данил Трегубов
Yêu cầu Android
Android 4.1+
Danh mục
Báo cáo
Sheikh Jafar - Sharhin Kashf ush-Shubuhaat Mp3
2.1 by first-rate-apps
Nov 3, 2019