下载 APKPure App
可在安卓获取Tafsir 3 - Sheik Jaafar Mahmud Adam MP3的历史版本
塔夫西尔3 - 谢赫贾法尔·马缪德亚当MP3下线
Assalama - Alaikum:
wannan Application mai suna " Sheik Ja'afar Tafsir Series ." yana dauke da tafsir na sheik jaafar mahmud adam wanda yayi a maiduguri
Baya ga haka wannan manhaja mun rabashi zuwa kashi 17 saboda nauyi dayake dashi ...saboda haka akoda yaushe mutum zai iya dauko sauran idan ka shigo play store kayi searching na username namu
Dadi da kari munyi application na sheik jaafar dayawa kamar haka:
.Tambayoyi dubu na sheik jaafar
.tambayoyin aure na sheik ja'afar
.kitabu tauhid by sheik jaafar
.bulugul maram na sheik jaafar
Takaitaccen tarihin Marigayi sheik jaafar
An haife shi ranar 12 ga watan Fabrairu shekarar1960, a garin Daura cikin jahar Katsina a Nijeriya.
Yayi karatun Al-qur'ani a gidansu a wurin mijin yayarsa wato Malam Haruna. Daga nan sai aka kawo shi unguwar Fagge a Kano wurin Malam Abdullahi, ya fara haddar Alkur'ani a gida sannan ya kammala anan Kano a 1978. Daga nan sai Malam ya shiga makarantar Arabic school karkashin cibiyar Egyptian CulturalCenter dake Bello Dandago Road a 1981. A wannan lokaci, Malam yana zuwa makarantar Adult School dake Shahuci, da daddare, ita kuma Egyptian Centre da yamma.
Ya kammala a shekarar 1984, wannan ya bashi damar shigaGovernment Arabic Teachers College Gwale a 1984, ya kammala a 1988. Daga nan ne kuma Malam ya samu shiga Jami'ar Musulunci ta Madina a 1989 zuwa 1993. Daga cikin Malamansa akwai Sheikh Abdul Rafi'i, Dr. Mahmud Abdul Haliq sai Dr. Khald As-Sabat.
Bayan Malam ya dawo daga Madina ya cigaba da karatu a Jami'ar Bayero daga baya wasu matsaloli suka hana shi cigaba. Amma a halin yanzu yana yin digirinsa na biyu a 'InternationalUniversity of Africa', dake Sudan.
Bayan Malam ya dawo daga Madina ne ya kafa Makarantar Usman Bin Affan daga nan ta samu cigaba ta zama cibiya mai zaman kanta a 1995. Sai darussa da Malam yake gabatarwa anan Usman bin Affan, na farko akwai karatun tafsiri ya da yake gabatarwa a ranar jumma'a tsakanin magariba da isha'i, ranar asabar karatun nahawu da balaga da safe da misalin 8:00am zuwa 9:30am. Sannan kuma karatun sirah ranar lahadi a
Masallacin Almuntada dake Dorayi tsakanin magriba zuwa isha'I, sai laraba kuma da yake gabatar da tafsiri a Masallacin Beirut, tsakanin magriba zuwa isha'i da kuma darussan da Malam yake gabatarwa a makaranta.
Bayan haka, Malam yana gabatar da tafsiri a Maiduguri a watan Azumi kuma shekara tara kenan da farawa.
A halin yanzu Malam shine shugaban cibiyar Usman Bin Affan Islamic trust kuma limamin jumma'a na Masallacin Almuntada dake dorayi a Kano.
Malam yana cikin mambobin kwamitin Malamai wato "Ulama Consultative" Zamfara State da Bauchi State. Haka kuma, Malam yana gabatar da shirye shirye a gidajen radio da talabijin da yawa, amma kadan daga cikinsu akwai na Radio Kaduna, Bauchi Radio corporation, CTV Kano, dana DITV Kaduna NTA Borno, OITV Damaturu, FM Andaza kiyawa ,Radio Jigawa,NTA Yola, da sauransu.
Malam yana da iyali ( mata biyu) da 'yaya (biyar) kuma yana zaune ne a unguwar Gadon kaya cikin birnin Kano.
malam ya rasu 13 gawatan April 2007 sakamakon harbinsa da akayi yana sallah a masallaci
Muna Addu'ar Allah yagafartamasa ,Allah kuma yasa aljannah itace makomarsa...Ameen
Last updated on 2017年10月29日
Minor bug fixes and improvements. Install or update to the newest version to check it out!
Tafsir 3 - Sheik Jaafar Mahmud Adam MP3
1.0 by TIN S2 BELLA
2017年10月29日